Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga ma’aikatar lafiya ta kasar ta karfafa dokar bada magani domin sanya ido kan sayar da magunguna barkatai a Najeriya.
Majalisar, ta bukaci majalisar kula da magunguna ta kasa ta dauki matakin gaggawa na rufe kamfanonin samar da magungunan da suka sabawa doka ciki hadda wuraren sayar magunguna na kasuwanni.
Ta umarci ma’aikatar lafiya ta kasa ta tabbatar magungunan da kwararrun ma’aikatan lafiya suka rubuta ake baiwa marasa lafiya, tare da rufe wuraran sarrafa magunguna wadanda basu da inganci.
Majalisar ta kuma bukaci hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC da su yi aiki tare da kungiyoyi masu zaman kan su da ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a wajen wayar da kan jama’a illar ta’ammali da muggan kwayoyi.
Sannan ta dorawa kwamitin kula da miyagun kwayoyi,lafiya da walwalar jama’a alhakin tabbatar an bi wannan doka.