Majalisar dokokin jihar Kano ta yi zama na musamman domin yin gyara ga wasu dokoki guda uku da suka hada da dokar ‘yan fansho, dokar hukumar ayyukan Majalisa da kuma dokar Kula da kudaden bangaren shariah.
Yayin Zaman Majalisar, an amince da gyaran shekarun ritaya na ma’aikatan gwamnati jihar Kano daga shekaru 40 na aiki zuwa 35 na ritaya kamar yadda yake a baya.
Sai Kuma shekarun haihuwa daga shekaru 65 ya zuwa shekaru 60 na haihuwa.
In za a tuna tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ce tayi gyaran dokar tare da Karin shekarun biyar ga ma’aikatan gwamnatin jihar lokacin ritaya.
Haka zalika ita ma dokar da ta shafi hukumar kashe kudaden ayyukan shariah an cire ta, tare da mayar da ita karkashin humakar fansho ta jihar.
A jawabin da Mai magana da yawun Shugaban Majalisar dokokin jihar kamaluddeen Sani Shawai ya futar ga manema labarai ya Kara da cewar majalisar ta rage shekaru 5 ne kawai.
Haka kuma Shugaban kwamitin harkokin zabe na Majalisar dokokin jihar Kano Hon, Muhammad Murtala Kadage ya mika rahoton kwamitin kan tantance sunayen kwamishinonin hukumar zabe ta jihar Kano guda 7 domin tantancewa.