LIKITOCI DUBU 55 NE KE KULA DA MARASA LAFIYA A NAJERIYA

11

Gwamnatin tarayya tace Likitoci masu lasisi 55,000 ke kula da marasa lafiya masu yawa a kasar nan biyo bayan ficewar kwararrun ma’aikatan lafiya zuwa kasashen ketare domin neman wani aikin.

Ta kara da cewa a shekaru 5 da suka gabata,akalla likitoci dubu 15 zuwa dubu 16 ke yin kaura zuwa kasashen waje.

Ministan lafiya Farfesa Ali Pate shine ya bayyana haka a gidan Talabijin na Channels.

Ali Pate,ya jadadda kudirin gwamnatin tarayya na fadada shirin horaswa da zuba jari domin dawo da likitocin da suka zabi su dawo domin yin aiki a gida Najeriya.

Ministan lafiyan yace akwai kwararrun ma’aikatan lafiya 300,000 a kasar nan, amma guda 55,000 ne kadai likitoci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six + 16 =