KINGSLEY MOGHALU YA YABA DA MATAKIN SHUGABA TINUBU NA JANYE TALLAFIN MAN FETIR

13

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya CBN Kingsley Moghalu, ya yaba da matakin shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya dauka na janye tallafin Man Fetir da yin garambawul a tsarin canjin kudade.

Kingsley Moghalu, wanda ya bayyana damuwa dangane da shigar da ‘Yan siyasa masu yawa cikin gwamnati, ya bukaci shugaban kasar ya yiwa majalisar zartarwa gwamnatin sa garambawul a shekarar farko ta wa’adin gwamanatin sa.

Ya fadi haka ne a wurin babban taron shugabanni karo na goma sha shida na wannan shekara da yake gudana a otel din Transcorp Hilton dake Abuja.

A halin da ake ciki kuma tsohon mataimakin Gwamnan babban bankin wanda kuma shi ne shugaban sashin sauye-sauyen tasarrafin kudi mai dorewa na bankin, Kingsley Maghalu yace rancen naira tiriliyan talatin karkashin tsarin karbo rance na WAYS AND MEANS da gwamnatin tarayya tsarin cin hanci ne tsagwaro.

Idan za’a iya tunawa tsohuwar gwamnatin shugaba Muhamamdu Buhari ce  ta karbo rancen fiye da Naira Tiriliyan 22 karkashin tsarin karbo na WAYS AND MEANS daga babban bankin kasa CBN, sannan aka sake karbo bashin Naira Tiriliyan 7 a lokacin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu mai ci yanzu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − one =