GWAMNATIN TARAYYA ZATA FARA BINCIKE KAN JAMI’O’I MASU ZAMAN KAN SU

4

Gwamnatin tarayya ta nemi jin ra’ayoyin jama’a yayin da ta fara bincike kan jami’o’I masu zaman kan su da aka kafa shekaru 15 da suka gabata.

Gwamnatin tarayya ta fara wannan binciken ne biyo bayan wani rahoton bincike da dan jaridar Jaridar Daily Nigerian Umar Audu ya gabatar,na bankado badakalar shedar kammala digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo mai makwabtaka.

Binciken da manema labarai suka yi ya nuna jami’o’I masu zaman kansu akalla 107 da aka kafa shekaru 15 da suka gabata binciken zai shafa.

Kwamitin binciken da gwamnatin tarayya ta kafa zai yi bincike kan jami’o’I da aka kafa shekaru 15 da suka gabata, domin duba yanayin tsari shugabannin jami’o’in, isassun kudaden shiga,abubuwan da suka zama wajibi,masu koyarwa da sauran su.

A rahotan bincike da dan jaridar Daily Nigeria Umar Audu ya gabatar ya nuna yadda ya samu kwalin digiri a kasar Benin cikin makonnin shida kacal, sannan ya dora da yin hidimar bautar kasa NYSC.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × three =