
Gwamnatin tarayya ta dage kaddamar da shirin bada lamunin karatu ga dalibai sai abinda hali yayi.
Shugaban asusun bada lamunin karatun dalibai na kasa Akintunde Sawyer, shine ya sanar da haka yayin tattaunawa da gidan Talabijin na ARISE.
A watan Yunin shekarar 2023 ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar bada lamunin karatu domin daliban Najeriya dake karatu a manyan makarantun gaba da sakandire su samu rancen kudin karatu maras ruwa daga gwamnatin tarayya.
Tsohon kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, shine ya gabatar da kudirin dokar wanda aka tsara zai fara aiki tsakanin watan Satumba da Oktobar shekarar 2023.
A halin da ake cikin, shugaban kasa Tinubu yace a watan Janerun wannan shekara 2024 shirin zai fara aiki bayan da aka gaza fara shi a watan Oktoba.
Kazalika,awanni 48 kafin kaddamar da shirin shugaban asusun bada lamunin karatu na kasa Akintunde Sawyer, yace an dage kaddamar da shirin saboda wasu gyare-gyare da aka yi dab da kaddamar da shirin.
