GWAMNATIN NAJERIYA TA GARGADI KAMFANONIN RARRABA WUTAR LANTARKI DANGANE DA KARANCIN WUTA LANTARKI

7

Gwamnatin tarayya tace Kamfanonin rarraba wutar lantarki zasu fuskanci hukunci kan matsalar karancin wutar lantarki a kasar nan.

Ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu yayi barazanar saka tukunkumi ga Kamfanonin cikin hadda soke musu lasisi,tare da nuna matukar damuwar sa dangane da karancin wutar lantarki da ake fama da shi a Najeriya.

Mista Adelabu,ya gayyaci kamfanonin rarraba wutar lantarki na Abuja da kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan da kuma Kamfanin samar da wutar lantarki na kasa TCN domin su yi ganawar gaggawa.

Ministan ya nuna rashin jin dadin sa bisa karancin ayyukan kamfanonin wajen samar da wutar lantarki a Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 4 =