Gwamnatin Najeriya na duba yuwuwar karbar bukatar kasashen waje domin tallafa mata a yakin da ta keyi da masu garkuwa da mutane dakuma sauran manyan laifuka
Dayake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar zartarwa na wannan makon bisa jagorancin shugaban kasar, Ministan yada labarai da wayar da kai Mohammed Idris, yace Amurka da wasu kasashe sun nuna sha’awarsu ta shiga wannan yakin
Ministan wanda bai bayyana sauran kasashen ba, ya jadda bukatar shuban kasa kan umarnin jami’an tsaro su maido da duk mutanen da suke hannun ‘yan bundiga