Gwamnatin kasar Venezuela ta shirya gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 28 ga watan Yuli na wannan shekara.
Shugaban kasar Nicolas Maduro, wanda ke shugabancin kasar tsawon shekaru 11 ya bayyana a fili cewa ana sa ran zai sake neman shugabancin kasar.
A shekarar data gaba ne,gwamnatin kasar da kuma bangaran adawa a kudancin Amurka suka amince a gudanar da zaben shugaban kasar a wannan shekara tare da gayyato masu sa ido daga kasashen duniya.
A zabuka da suka gudana a shekarar 2018, lokacin da aka bayyana Mista Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben ‘Yan kasar sun bayyana shakkun kan sahihancin zaben.