Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce zata ciyar mutane 171,900 kowacce rana a lokacin watan Azumin Ramadan.
Gwamna Malam Umar Namadi,wanda ya fadi haka yayin kaddamar da rabon kayan tallafi a babban birnin Jiha Dutse,yace gwamnatin Jiha ta himmatu da ciyar mutane 5,157,000 har watan Azumi ya kare.
Yace tuni aka samar da cibiyoyi guda biyu a kowacce mazaba domin gudanar da wannan shirin,yana mai cewa ana kyautata zaton kowacce cibiya daya za’a ciyar da mutane akalla 300 kowacce rana,adadin mutanen da za’a ciyar ya kai 171,900 a cibiyoyi 573 a rana guda.
Gwamna yace an tsara shirin ne domin ciyar da mutane gama gari a dukkanin cibiyoyin,inda ya kara da cewa za’a shigar da dubban magidanta cikin shirin ciyarwar.
Malam Namadi,yace wanna shirin zai taimakawa mutane mabukata a lokacin watan Azumin Ramadan.
Tunda farko,kwamishinan ayyuka na musamman na Jihar Jigawa Auwalu Sankara,yace za’a rabawa kimanin mutane 150,000, buhunan shinkafa 150,000 da buhunan masara 150,000 da katan 100,00 na taliya.
Auwalu Sankara yace mutane 700,000 a fadin kananan hukumomi 27 na Jihar jigawa da mutane 5 daga kowanne gida ake tsammanin zasu amfana da wannan tallafi.