Fadar shugaban kasa ta musanta zargin yin aringizon Naira Tiriliyan 3 kari kan kasafin kudin shekarar 2024.
Wannan ya biyo bayan zargi da dan majalisar Dattawan Sanatan Abdul Ningi, daga Jihar Bauchi yayi cewa majalisar zartawa na amfani da kasafin kudi fiye da wanda aka amince da shi ranar 1 ga watan Janerun shekarar 2024.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dattawan ta ce za ta gana kan lamarin a ranar Talata.
Abdul Ningi,ya zargi gwamnatin tarayya karkashin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da yin amfani da kasafin kudi fiye da wanda aka gabatarwa majalisar dokokin kasar nan.
A cewar dan majalisar dattawan,Naira Tiriliyan 25 aka amince da shi a matsayin kasafin kudin shekarar 2024, amma yanzu gwamnatin tarayya na yin amfani da Naira Tiriliyan 28.7 a matsayin kasafin kudin.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar,fadar shugaban kasa ta bayyana wannan zargin na Abdul Ningi a matsayin karya,dake cewa tunda farko shugaban kasa ya gabatarwa majalisar dokokin kasa Naira Tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin kudi.