
Kisan gillar da aka yiwa babban Limamin masallacin Juma’a na garin Mada dake karamar hukumar Gusau ta Jihar Zamfara Imam Abubakar Hassan Mada, ya haifar da cece-kuce a Jihar.
Majiyoyi daga makusanta marigayin da suke nemi a sakaye sunan su,tace a ranar Lahadi ne wasu ‘Yan sakai su 5 suka shiga kauyen akan Babura inda suka tafi da limamin.
Majiyoyin sun kara da cewa ‘Yan sakan sun umarci limamin ya hau daya daga cikin baburan,bayan sunyi ‘yar tafiya kadan daga garin na Mada suka kashe shi.
Ganau sun bayyana cewa Limamin na zaune a kofar gidan sa bayan sallar La’asar a lokacin da ‘Yan sintirin suka kama shi.
