Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Legas ta tsaurara matakan tsaro a shagunan sayar da kayayyaki da rumbunan adana kayan abinci na gwamnati domin gudun kai farmaki wuraran.
Haka kuma jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA a yankin Kudu maso Yamma, sun ce an tsaurara matakan tsaro a rumbunan adana kayan abinci dake yankunan domin kada a kai musu hari.
An dauki wannan mataki ne domin kare wuraren ajiyar kayan abinci na gwamnati da shagunan sayar da kayayyaki, saboda kare su daga batare dake kaiwa wuraren hari sanadiyyar matsin rayuwa da yunwa da suka barke a kasar nan.
Idan dai za’a iya tunawa, wasu bata gari sun kai farmaki wurin adana kayan abinci na gwamnati dake Dei-Dei a karamar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja,inda suka kwashe abinci mai dimbin yawa.