ADADIN WADANDA SUKA MUTU A JIHAR BENUE SAKAMAKON KAMUWA DA CUTAR SANKARAU YA KAI MUTANE 13

10

Gwamnatin Jihar Benue tace adadin wanda da suka mutu ya kai mutane 13 sakamakon barkewar cutar zazzabin Lassa duk da kokarin da gwamnatin Jihar ke yi na dakile cutar.

Rahotanni sun ce mutane 9 sun rasu sakamakon barkewar cutar a wasu sassan Jihar.

Sai dai kuma an sake samun karin mutuwar mutane hudu cikin kwanaki biyu da suka wuce wanda adadin wadanda suka rasu ya kai mutane goma sha uku.

Kwamishinan lafiya da kyautata rayuwar al’umma na Jihar Dakta Yanmar Ortese, ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Makurdi babban birnin Jihar,inda jadadda bukatar wayar da kan al’umma domin dakile yaduwar cutar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × three =