Za a yiwa yara rigakafin zazzabin cizon sauro zuwa karshen 2023 – WHO

23

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) tace za a raba sabbin alluran rigakafin zazzabin cizon sauro dayawa daga shekarar 2023 domin kare miliyoyin yaran dake kasashen da cutar tafi kamari.

Abdisalan Noor ma’aikacin shirin zazzabin cizon na WHO a yau yace sama da kasashe 20 ne suka shirya amfani da alluran rigakafin kuma wasu za su fara amfani da su zuwa karshen shekarar 2023.

Yace wasu gwamnatoci za su samu alluran tare da tallafin hadakar bayar da agajin alluran rigakafi ta duniya.

Kamar yadda yazo a wani kiyasi na hukumar ta WHO, mutane dubu 619 ne suka mutu sanadiyyar zazzabin na cizon sauro a fadin duniya a shekarar 2021, kasa da mutane dubu 625 da suka mutu a shekarar 2020.

Hukumar ta WHO a rahotonta na zazzabin cizon sauro na shekara-shekara tace wadanda ke dauke da cutar sun kai miliyan 247, amma ana samun raguwar wadanda ke harbuwa.

Rahoton ya kara da cewa kimanin kashi 95 na wadanda ke kamuwa da wadanda ke mutuwa a nahiyar Afrika su ke.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 + three =