Za a dawo jigilar jirgin kasan Abuja-Kaduna a Disamba – Gwamnati

21

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a ci gaba da jigilar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 5 ga watan Disamba.

Manajan daraktan hukumar kula da sufurin jiragen kasa na kasa, Fidet Okhiria, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa a jiya cewa, an shirya komai domin dawo da jigilar.

Fidet Okhiria, a saboda haka, ya shawarci fasinjojin da ke son amfani da jiragen kasan da su sabunta manhajojinsu na wayar hannu tun daga ranar 3 ga Disamba, domin ba su damar hawa jiragen.

Fidet Okhiria ya baiwa fasinjojin hukumar tabbacin cewa gwamnatin tarayya ta dauki alkawarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin da ke cikin jiragen kasan a koda yaushe.

Kamfanin Dillancin Labaran ya bayar da rahoton cewa, Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, a yayin gwajin jirgin kasa ranar Lahadi ya ba da umarnin cewa ‘yan Najeriya da ba su da lambar shaidar zama ‘yan kasa ta NIN ba za su shiga jiragen ba.

Ministan ya ce an kammala kashi 90 cikin 100 na matakan tsaro da za a bi kafin a fara jigilar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − 10 =