‘Yansandan Ghana sun haramta sanar da sakonnin wahayin sabuwar shekara

11

‘Yan sanda a Ghana sun gargadi malaman addinai game da sanar da sakonnin wahayi na sabuwar shekara da ka iya haifar da tsoro, damuwa ko mutuwa.

Rundunar ‘yan sandan a cikin wata sanarwa ta ce bai kamata ‘yancin yin addini ya keta hakkin wasu ba.

Masu suka dai sun ce wannan umarni ya saba wa ‘yancin yin addini da tsarin mulki ya bayar, a saboda haka ya sabawa doka.

Miliyoyin Kiristoci sukan taru a coci-coci don su ji fastocinsu suna sanar da sakonnin wahayin sabuwar shekara.

Sau da yawa sakonnin suna fitowa ne daga hasashe masu kyakkyawan fata zuwa wadanda ke gargadin halakar da ke tafe.

Umurnin ‘yan sandan ya fara aiki ne a shekarar da ta gabata bayan da jama’a suka yi hasashen macece da bala’o’i.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 2 =