‘Yan majalisar Nijar na neman haramta alaka tsakanin jinsi daya

40

Wasu gungun ‘yan majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar sun goyi bayan wani kudiri na neman haramta alaka tsakanin jinsi daya a kasar.

Mafi akasarin al’ummar Nijar musulmi ne, amma kasar tana da gwamnati da ba ruwanta da addini kuma a halin yanzu babu takamaiman dokar da ta shafi alaka tsakanin jinsi guda.

‘Yan majalisar sun ce dangantakar jinsi daya ta sabawa akidar addini da al’adun mutane.

‘Yar majalisar, Nana Djibou Harouna, mai wakiltar yankin kudancin Maradi ce ta gabatar da shawarar ga kakakin majalisar.

Ta shaida wa taron manema labarai jiya a Yamai babban birnin kasar cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare hakki da muradun jama’a.

Nana Djibou Harouna ta bayyana alaka tsakanin jinsi daya a matsayin matsalar da ke damun al’umma.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 3 =