Wasu ma’aikatan gwamnati sun fi Buhari albashi – Shehu

34

Shugaban hukumar tara kudaden shiga da tsara albashi ta kasa, Muhammed Shehu, yace wasu ma’aikatan gwamnati suna karbar albashin wata-wata wanda yafi na shugaban kasa Muhammadu Buhari yawa.

Muhammed Shehu ya sanar da haka yau yayin wata fira a gidan talabijin na Channels.

A cewarsa, wasu ma’aikatan hukumomin gwamnati irinsu hukumar kula da sufurin jiragen ruwa (NIMASA), hukumar sadarwa ta kasa (NCC), hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa (NPA) da babban bankin kasa (CBN), da sauransu, na daukar albashi fiye da na shugaban kasa.

Yayi nuni da cewa hukumar NPA na daya daga cikin hukumomin da suka fi kowanne samar da kudaden shiga a bana, inda ya kara da cewa hukumar ta tara kudaden shiga na sama da naira miliyan dubu 172 a watanni shidan farkon shekarar 2023.

Yace Najeriya na da kashe-kashen albashi kimanin 17 a hukumomi daban-daban. Sai dai, ya bayar da shawarar daidaita albashin ma’aikatan gwamnati.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 5 =