Sojojin Congo sun zargi ‘yan tawaye da kashe fararen hula 50

25

Sojojin Congo sun zargi ‘yan tawayen M23 da kashe fararen hula kusan 50 a garin Kishishe da ke gabashin kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin kashe-kashen jama’a bayan sake barkewar fada, inda yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka amince da ita a makon da ya gabata ke nuna alamun rugujewa.

Kungiyar ‘yan tawayen dai ta musanta zargin da ake musu, tana mai cewa ba ta taba kai wa fararen hula hari ba

Dubban mutane ne ke tserewa fadan da ake gwabzawa tsakanin ‘yan tawaye, da dakarun gwamnati da kuma mayakan sa-kai a sassa daban-daban na lardin Kivu ta Arewa.

Rwanda da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo sun amince a tattaunawar da suka yi a Angola cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta za ta fara aiki a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kungiyar M23 ta ce tsagaita wutar ba ta shafe su ba domin ba a gayyace su zuwa tattaunawar ba.

Rwanda ta musanta zargin cewa tana goyon bayan kungiyar ‘yan tawayen ta M23.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × one =