
Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta fitar da shawarwarin kiwon lafiyar jama’a a kasar, biyo bayan amincewar da shugaban kasa yayi na sassauta dokokin kariya daga corona da matakan bulaguro ko dawowa daga kasashen waje.
Darakta Janar na hukumar, Dr Ifedayo Adetifa, yau a Abuja ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa hakan na zuwa ne sanadiyya raguwar masu kamuwa da corona da kuma yawan karuwar wadanda ake yiwa rigakafin corona a kasar.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sassauta dokokin kariya daga corona da matakan bulaguro ko dawowa daga kasashen waje ba tare da bata lokaci ba, biyo bayan shawarar da kwamitin corona na shugaban kasa, bisa la’akari da shaidar asibitoci da ke tabbatar da raguwar kamuwa da corona a fadin kasarnan.
Shawarwarin kiwon lafiyar sun hada da dage matakan dakile corona domin matafiya, da janye amfani da kyallen rufa fuska bisa tilas a wuraren taruwar jama’a da hana dandazon jama’a.
Sanarwar hakan na zuwa ne ta bakin sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin corona na shugaban kasa, Boss Mustapha.