NANS za ta fara zanga-zangar neman sakin Aminu Mohammed

32

Kungiyar dalibai ta kasa NANS, ta ce za ta fara wata zanga-zangar sai baba ta gani a fadin kasarnan, domin neman a sako wani dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, Aminu Mohammed, wanda aka kama aka kuma kai shi gidan yari a kan wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter yana sukar uwar gidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya mai dauke da sa hannun shugabanta, Usman Barambu, kungiyar ta bayyana cewa za a fara zanga-zangar ne a ranar Litinin mai zuwa har sai Aminu Mohammed ya samu ‘yanci.

An ruwaito cewa a baya kungiyar dalibai ta kasa ta nemi afuwar uwargidan shugaban kasar kan abin kunyar da Aminu Mohammed ya wallafa a shafinsa na twitter da ya janyo mata damuwa da iyalanta, yayin da ta kuma bukaci a saki dalibin.

Sai dai kungiyar ta bayyana cewa ta gaji da bin hanyar lallami da sulhu, a saboda haka za ta fito da karfinta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 + eleven =