Najeriya za ta samu kujerun aikin hajji dubu 90 a 2023

24

Masarautar Saudiyya ta sanar da cewa za ta dawo da adadin kujerun hajjin da aka baiwa Najeriya kafin corona.

Idan za a iya tunawa, an dakatar da aikin hajjin ga matafiya na kasashen waje a shekarun 2020 da 2021 yayin da a aikin hajjin bara aka rage yawan mahajjata zuwa rabi.

Wannan ya sa Najeriya ta samu rabin kujeru guda dubu 45, daga cikin kujerun da aka ware mata a baya guda dubu 90.

Mataimakin daraktan yada labarai da sadarwa na hukumar alhazai ta kasa, Mousa Ubandawaki a wata sanarwa da ya fitar yau ya bayyana cewa babban darakta mai kula da alhazan Saudiyya a ma’aikatar Hajji da Umrah Bahauddeen bin Yusuf Alwani ne ya bayyana hakan.

Bahauddeen bin Yusuf yayin wani taron share fage na aikin hajjin 2023 ta hanyar bidiyon kai tsaye tare da Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa, Alhaji Zukrullah Kunle Hassan ya kara da cewa ka’idojin da ma’aikatar ta fitar na aikin Hajjin 2023 sun hada da cire kayyade shekaru da soke cutar gwajin cutar corona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven − ten =