Na cika dukkan alkawarukan da na daukawa Jigawa – Badaru

12

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ayyana cewa ba shi da dana sani a wa’adi biyu na mulkinsa kasancewar mutanen jihar har yanzu suna kaunarsa da girmama shi.

Gwamnan wanda ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a ofishinsa, yace ya aiwatar da akalla aiki daya a dukkanin kauyukan jihar.

Gwamna Badaru yace ya cika dukkan alkawarukan da ya dauka yayin yakin neman zabe har ma da karin wasu ayyukan cigaba wadanda suka inganta walwala da tattalin arzikin mutanen jihar Jigawa.

Yace yanzu jihar Jigawa ce ta daya a bangaren samun ruwan sha a Arewacin Najeriya, inda ta kasance ta biyu a kasarnan.

Ya kara da cewa kayayyakin amfanin gona da ake samarwa a jihar Jigawa sun ninku yayin da aka samu cigaba da kaso 60 a bangaren ilimi kuma ma’aunin tattalin arziki GDP na jihar ya rubanya a karkashin mulkinsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 − one =