Mun tafka asarar N20b cikin watanni 3 – ‘Yan jari bola

33

Kungiyar ‘yan jari bola ta kasa ta koka kan cewa mambobinta sun tafka asarar kimanin naira miliyan dubu 20 cikin watanni uku.

Shugaban kungiyar mai kula da yankin Arewa, Aminu Soja, shine ya sanar da hakan yayin wani taro na wuni guda da aka gudanar jiya a Kano.

Aminu Soja yace har yanzu mambobin kungiyar na lissafa asarar da suka tafka sanadiyyar rashin daidaiton farashi daga masu sayen kayayyakinsu.

A cewarsa, cikin watanni biyun da suka gabata, suna sayar da ton 1 na karfe akan kudi naira dubu 350, amma kamfanonin da suke saya sun karya farashin zuwa naira dubu 270 kowane ton 1.

Sai dai, shugaban kungiyar yace kamfanonin sun bayyana ambaliyar ruwa da yanayin damina a matsayin dalilan da suka jawo rashin daidaiton farashi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 4 =