Majalisar Wakilai ta barranta kanta da Gudaji Kazaure akan batun kudade

9

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya nesanta majalisar daga takaddamar kudaden harajin da ake yi tsakanin dan majalisar, Gudaji Kazaure da wasu jami’an gwamnati.

Gudaji Kazaure, mai wakiltar Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi na jihar Jigawa ya yi ikirarin cewa sama da naira tiriliyan 89 na harajin kudade stamp dunty sun bata.

Dan majalisar ya yi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin sakataren kwamitin shugaban kasa na sasantawa da dawo da dukkan kudaden harajin.

Gudaji Kazaure ya kuma zargi gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emeifele, tare da hadin bakin wasu jami’an gwamnati, da kokarin dakile yunkurin kwamitin na kwato kudaden.

Amma da yake zantawa da wakilin fadar shugaban kasa jiya bayan ganawarsa da shugaban kasa, Femi Gbajabiamilla ya ce Gudaji Kazaure da tawagarsa ba sa aikinsu domin majalisar.

Kakakin majalisar ya bayyana cewa, Gudaji Kazaure bai bata sunan majalisar ba ko ‘yan majalisar don haka babu matakin da za a dauka a kansa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two − 1 =