Majalisa ta nemi CBN ya dakatar da shirin kayyade kudade

36

Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin kasa, CBN, da ya dakatar da aiwatar da sabuwar manufar yawan kudaden da za a iya cirewa daga ranar 9 ga watan Janairun 2023.

Idan za a iya tunawa dai, babban bankin ya iyakance naira dubu 20 a kullum da kuma naira dubu 100 a mako a matsayin kudaden da mutum zai iya fitarwa.

Da suke mayar da martani, ‘yan majalisar wakilai a zamansu na yau, sun yi Allah wadai da wannan sabuwar manufar, inda suka gayyaci gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, domin yin bayani kan manufofin bankin na ‘yan kwanakin nan.

Kudurin dai ya biyo bayan wani kudiri ne na gaggawa da Magaji Da’u Aliyu na jam’iyyar APC daga jihar Jigawa ya gabatar.

Da’u Aliyu ya ce, wannan sabuwar manufar da CBN ta fitar na kayyade kudaden da za a rika fitarwa a kullum zuwa Naira dubu 20, bata dace ba, domin hakan zai yi illa ga ‘yan Najeriya, musamman masu gudanar da kananan sana’o’i.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − 11 =