Mabiyan malamin nan na Kano Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a karkashin inuwar Ashabul Kahfi Warraqeem reshen jihar Bauchi sun yanke shawarar daukaka kara kan hukuncin da wata kotun shari’ar Musulunci ta Kano ta yanke na hukuncin kisa ga malamin.
Da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Abdullahi Musa, ya yi zargin cewa siyasa ce ta gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ta jawo yanke hukuncin, inda ya kara da cewa Shehin Malamin na sukar Gwamna Ganduje.
Abdullahi Musa ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano da wasu malamai na kiyayya da Abduljabbar Kabara tare da hada kai domin yaki da shi.
Ya ce mabiyansa ba su da karfin kare shi a kotu su kadai, a saboda haka ya bukaci taimakon shari’a daga daidaikun jama’a da kungiyoyi.
Ya yi zargin cewa wasu daga cikin kungiyoyin addinan da a yanzu suka hada kai don kawar da Abduljabbar Kabara, su ne suke aikata batacin a addini a wa’azin da suke yi amma ba a yi musu komai ba.