JAMB ta sanar da ranakun rijista da jarabawar UTME da DE na 2023

21

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta amince da fara rajistar jarrabawar shiga manyan makarantu UTME ta shekarar 2023, daga ranar 24 ga watan Janairu zuwa 14 ga watan Fabrairu, 2023.

Hukumar ta kuma sanya ranar 16 ga watan Maris, 2023, domin gudanar da jarabawar gwaji ta UTME.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Dr Fabian Benjamin, ya fitar jiya a Abuja.

Fabian Benjamin ya ce hukumar, duk da haka, ba ta hada da rijistar DE ba a lokacin, kasancewar rajistar DE za ta fara ne daga ranar 20 ga watan Fabrairu zuwa 20 ga watan Afrilu, 2023.

Har ila yau, ya ce hukumar, bayan ta yi la’akari da sauran alkawurran ta, ta sanya ranar 29 ga watan Afrilu, 2023, don gudanar da jarabawar UTME ta shekarar 2023, kuma ana sa ran za ta kare a ranar 12 ga watan Mayun, 2023.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − seventeen =