Hukumar NDE ta raba bashi ga mata da matasa a Jigawa

54

Hukumar samar da ayyukan yi ta kasa (NDE) ta raba kudi naira miliyan 4 da dubu 300 a matsayin bashi ga mata da matasa marasa aikin yi su 43 a jihar Jigawa.

Darakta Janar na hukumar, Mallam Abubakar Nuhu Fikpo, shine ya sanar da haka lokacin aikin rabon bashin yau a birnin Dutse.

Nuhu Fikpo, wanda ya samu wakilin ko’odinetan hukumar na jiha, Miwa Lasco, yace kowane mutum ya samu naira dubu 100 domin fara sana’a ko ingantawa da fadadawa sana’arsa.

Ya bayyana cewa an zabo mutane 43 da aka bawa bashin daga cikin mutane 100 da aka basu horo tunda farko a wasu shirye-shirye guda 4, a karkashin shirin hukumar na koyar da sana’o’i da bayar da jari a yankunan karkara.

A cewarsa, an bayar da horon da nufin koyawa wadanda aka horas yadda za su iya dogoro da kawunansu tare da samar da ayyukan yi a bangaren aikin gona a al’umominsu.

Nuhu Fikpo ya kara da cewa shirin zai kuma taimaka wajen rage talauci tsakankanin al’umma.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 − 2 =