Gwamnatin Tarayya za ta sanar da karin albashi kwanannan

8

Ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, yace nan gaba kadan gwamnatin tarayya za ta sanar da karin albashin ma’aikatan gwamnati domin rage radadin hauhawar farashin kayan masarufi.

Ya sanar da haka lokacin da yake zantawa da manema labaran fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yace tuni kwamitin albashi na shugaban kasa ya fara bibiyar albashin kuma ana sa ran zai fitar da karin da za ayi a sabuwar shekara.

Idan za a iya tunawa dai, ‘yan kwanakinnan ministan yayi tsokacin cewa gwamnati za ta kara albashin ma’aikata domin magance wahalhalun da ake sha sanadiyyar hauhawar farashi.

Chris Ngige yace a shekararnan an sha fama da yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wanda aka fara a watan Fabrairu da kuma na wasu kungiyoyin da suka biyo baya, duka akan inganta yanayin aiki da karin albashi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + 3 =