Gwamnatin Jigawa za ta samar da karin tallafi ga wadanda ambaliya ta shafa

8

Gwamnatin jihar Jigawa zata bada kayayyakin tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya sanar da hakan a lokacin taron gangamin jamiyyar APC a garin Kiyawa a karamar hukumar Kiyawa ta jihar.

Yace gwamnati ta damu da halin da masu ambaliya suke ciki tare da fatan zasu dauki lamarin a matsayin kaddara daga Allah SWT.

Muhammadu Badaru Abubakar yana mai cewar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi alkawarin rubanya kudaden tallafin masu karamin karfi sau uku idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Gwamnan wanda kuma shine jagoran yakin neman zaben Tinubu da Shettima a arewacin kasar nan yace sake zabar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa zai bada damar dorawa akan aiyukan da Muhammad Badaru Abubakar ya bijiro dasu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + sixteen =