Gwamnatin Jigawa ta fara aiwatar da dokar kare yara

73
Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar

Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da kwamitin tabbatar da kare yara na jihar.

Sakataren gwamnatin jiha Abdulkadir Fanini ne ya kaddamar da kwamitin a Dutse babban birnin jihar.

Sakataren gwamnatin wanda kwamishiniyar harkokin mata ta jihar, Hajiya Yelwa Da’u ta wakilta, ta ce an kafa kwamatin ne domin tabbatar da aiwatar da dokar kare yara yadda ya kamata a jihar Jigawa.

Ta yi nuni da cewa ana tauye hakkin yaran, shi ya sa ake da bukatar kulawa sosai daga gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an kare hakkin yaran da ba su da gata.

Yelwa Da’u ta bukaci kwamitin da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansu tare da tabbatar da aiwatar da dokar kare yara yadda ya kamata a jihar.

A nata jawabin, shugabar ofishin hukumar kula da yara ta UNICEF a Kano, Amelia Allan, ta yabawa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, da majalisar dokokin jihar bisa yadda su ka tabbatar da amincewa da kudirin dokar kare yara ya zama doka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + two =