Gwamnatin Gambia tace ta dakile yunkurin juyin mulki

14

Gwamnatin kasar Gambia ta ce ta dakile yunkurin juyin mulki.

A wata sanarwa da aka fitar, an kama wasu sojoji hudu, yayin da wasu uku da ake zargi da hada baki suka gudu.

Sanarwar dai ba ta yi bayanin ko wanene ke da hannu a yunkurin hambarar da shugaba Adama Barrow a jiya ba, wanda ya sake lashe zabe karo na biyu a zaben da ya gabata.

Gambia kasa ce mai zaman lafiya a yammacin Afirka wacce ta shahara a wajen masu yawon bude ido saboda bakin teku da namun daji.

Adama Barrow ya doke shugaba Yahya Jammeh wanda ya dade yana mulki a zaben da aka gudanar a watan Disambar 2016.

An tilastawa Yahya Jammeh gudun hijira zuwa Equatorial Guinea, ko da yake ya kasance mai tasiri a Gambia, daya daga cikin kananan kasashen Afirka.

Babban birnin Gambia, Banjul, yana cikin kwanciyar hankali, inda rayuwa ke tafiya kamar yadda aka saba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × three =