Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya amince da biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30 ga ma’aikata a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Muhammad Umar, Babban Sakatare na ofishin shugaban ma’aikata ya fitar jiya a Bauchi.
A cewarsa, aiwatar da gyare-gyaren da zai biyo baya kan mafi karancin albashi zai fara ne daga kan ma’aikatan da ke mataki na 7 zuwa sama a matakin jiha da kananan hukumomi daga ranar 1 ga watan Disambar 2022.
Ya kuma ce gwamnan ya kuma amince da aiwatar da karin albashin karin girman ma’aikata a gwamnatin jiha da na kananan hukumomi daga ranar 1 ga watan Disambar 2022.
Muhammad Umar ya bayyana cewa gwamnati na kokarin ganin ta fara aiwatar da karin shekarun ritaya ga malaman makaranta a makarantun firamare da na sakandare a jihar.