Fafaroma zai kai ziyara Kongo da Sudan ta Kudu

20

Fafaroma Francis zai kai ziyara Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Sudan ta Kudu a farkon shekara mai zuwa.

A cewar wata sanarwa da fadar Vatican ta fitar, Paparoman zai ziyarci kasashen biyu tsakanin 31 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabrairu.

Sanarwar ta ce Paparoman zai samu rakiyar Archbishop na Canterbury da kuma mai gudanar da babban taron Cocin Scotland a Sudan ta Kudu inda zai shafe kwanaki biyu na karshe na tafiyar tasa.

Tun da farko an shirya tafiyar Paparoman zuwa kasashen biyu ne a watan Yulin wannan shekara amma an soke saboda matsalar rashin lafiyarsa.

Shugabanin kasashen biyu ne za su karbi bakuncinsa, sannan kuma zai gana da limamai da sauran malamai da kuma na kungiyoyin fararen hula na kasashen biyu.

A Sudan ta Kudu kuma ana sa ran zai gana da ‘yan gudun hijira a cikin kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 5 =