An kama wadanda ake zargi a rikicin makiyaya da manoma a Jigawa

66

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa a yau ta ce ta kwato shanu 11 da aka sace daga wani kauye bayan wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Takazza da ke karamar hukumar Guri ta jihar.

Mazauna yankin sun ce akalla mutane shida ne suka samu raunuka, an kuma yi awon gaba da shanu da dama da kuma kone-kone a rumbuna, biyo bayan wani rikici da ya barke a ranar Talatar makon jiya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Effiom Ekot, ya shaidawa manema labarai cewa, bayan afkuwar lamarin, rundunar ta kwato akalla shanu 11 da aka a sace a kauyen.

Effiom Ekot ya ce masu bincike suna aiki domin ganin an kwato shanu 16 da aka sace daga kauyen.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce an kwato shanun a wurare daban-daban.

Kwamishinan ya ce al’amura sun dawo daidai a kauyen Takazza kuma an tura jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × one =