An kama mutane 25 a wasu sumame a fadin kasar Jamus bisa zargin kitsa kifar da gwamnati.
An rawaito cewa wata kungiyar masu tsatsauran ra’ayi da tsaffin jagororin sojoji sun kitsa mamaye ginin majalisar dokokin kasar domin kwace mulki.
Ana zargin wani mutum mai suna Heinrich na 13 da zama jigo a shirye-shiryen kwace mulkin.
A cewar masu gabatar da kara na tarayya, yana daya daga cikin jagogorin kungiyoyin da aka kama a fadin jihohin Jamus 11.
An bayar da labarin cewa wadanda suka kitsa juyin mulkin mambobi na wata kungiyar masu tsatstsauran ra’ayi, wacce tun dadewa yansandan Jamus ke zargi da kai hare-haren ta’addanci da yada jita-jitar wariyar launin fata. Kazalika ‘yan kungiyar sun ki amincewa da kasar ta Jamus a yanzu.
Sauran wadanda ake zargin ‘yan wata kungiya ne wadanda suka yi amannar cewa kasarsu na hannu wadanda ke amfani da asiri wajen juya alakar gwamnati.