Tsohon Firai-Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na neman komawa mulki

19

Tsohon Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na yunkurin komawa kan karagar mulki.

A yau ne al’ummar Isra’ila ke komawa rumfunan zabe domin zaben kasar karo na biyar cikin kasa da shekaru hudu.

Kasar dai ta fada cikin wani yanayi na tabarbarewar siyasa da ba a taba ganin irinsa ba tun a shekarar 2019, inda aka tuhumi shugaban da ya fi dadewa kan karagar mulki da laifin cin hanci da zamba da cin amana, lamarin da ya musanta.

An tilastawa Benjamin Netanyahu murabus daga mukaminsa a tsakiyar shekarar 2021, lokacin da dan siyasa mai tsattsauran ra’ayi Yair Lapid ya hada wani kawance mai ban mamaki tare da jam’iyyun masu sassaucin ra’ayi da na Larabawa.

Gwamnatin da aka kafa ta zarce tsammanin mutane da dama, amma a karshe ta rushe a watan Yuni.

Yair Lapid a yanzu shi ne firaministan rikon kwarya kuma babban abokin hammaya a takarar Benjamin Netanyahu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 1 =