Najeriya na fuskantar hadarin shigowar Ebola – NCDC

43

Gwamnatin tarayya ta ce kasarnan na cikin hadarin shigowar cutar Ebola daga kasashen waje sakamakon barkewar cutar a kasar Uganda.

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce babban hadarin da kasar ke fuskanta na da nasaba da yawan zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da Uganda da kuma cakuduwar fasinjoji, musamman a wuraren tsayawar matafiya jiragen sama na biranen Nairobi, Addis Ababa da Kigali.

Hukumar ta kara da cewa, suna cikin shirin ko ta kwana, tare da daukar matakai da dama don yin rigakafi da dakile hanyoyin da ka iya haifar da barkewar cutar Ebola a Najeriya.

Wadannan matakan sun hada da kara sanya ido da tantance fasinjoji a tashoshin jiragen sama.

Hukumar ta kuma ba da shawara ga matafiya inda ta gaya wa ‘yan Najeriya da mazauna kasar cewa su guji duk wani balaguron da ba na tilas ba zuwa Uganda a yanzu har sai hukumomin kiwon lafiyar sun tabbatar da dakile bullar cutar a Uganda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 14 =