Adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da guguwa a kasar Philippines sun kai 150, yayin da mutane akalla 36 suka bata.
Hukumar kula da annoba ta kasar a yau ta ce jimillar mutane 128 ne suka jikkata.
Kusan mutane miliyan hudu ne iftila’in ya shafa wanda kuma sama da miliyan 1 da dubu 200 suka rasa matsugunansu.
Wuraren da abin ya shafa dai sun sha fama da ruwan sama na kwanaki da iska mai karfi da guguwa ta kawo, wadanda suka lalata gidaje sama da dubu 15.
An kiyasta lalacewar gonaki da ababen more rayuwa sama da dala miliyan 90 da dubu 900.
Shugaba Ferdinand Marcos Junior ya sanya larduna 23 da guguwar ta shafa karkashin dokar ta-baci na tsawon watanni shida masu zuwa, lamarin da zai baiwa hukumomi damar tara wasu kudade domin bayar da agaji da gyara inda suka lalace.
A wani labarin makamancin wannan, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce sama da mutane miliyan daya ne ambaliyar ruwa ta shafa sakamakon mamakon ruwan sama a kasar Sudan ta Kudu.
Ofishin ya ce aikin tallafin da yake yi tare da abokan huldarsa na samun cikas sakamakon sabbin tashe-tashen hankula, rashin tsaro da kuma rashin hanyoyi.
Lalacewar kayayyakin gwamnati kamar karyewar gadoji sun kara dagula lamarin, tare da rashin kudi.
An ba da sanarwar a yayin da wasu kafafen yada labarai ke cewa Uganda na iya bude madatsun ruwa a kogin Nilu domin rage yawan ruwan.
Ofishin ya kara da cewa, idan aka saki wannan ruwan to akwai yiyuwar al’amura su kara dagulewa a Sudan ta Kudu.
Hukumar ba da agaji da farfado da ayyukan jin kai ta gwamnati, ta tura tawagogin tantancewa zuwa yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kasar domin tattara karin bayanai kan bala’in da ambaliyar ruwa ta haddasa.