Jam’iyyar NNPP ta kaddamar da majalisar yakin neman zabe a Jigawa

127

Jam’iyyar NNPP a jihar Jigawa ta kaddamar da majalisar yakin neman zaben ta da kwamitoci gabanin babban zaben 2023.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na jihar Mutari Ibrahim Gonga, wanda aka rabawa manema labarai.

Ya ce majalisar yakin neman zaben ta na da dan takarar gwamna Malam Aminu Ibrahim Ringim a matsayin shugaba da Abdulaziz Usman Turabu a matsayin mataimakin shugaba.

Adamu Abunabo zai kasance sakataren kwamitin yakin neman zaben yayin da sauran su ne Mutari Ibrahim Gagarawa, Sanata Musa Bako, Alhaji Muhammed Garba da Alhaji Rabiu Isah Taura a matsayin mambobin majalisar.

Ya ce hukumar yakin neman zaben ita ce ke da alhakin daidaita dukkan ayyukan yakin neman zabe a fadin jihar.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a kaddamar da mambobin sauran kwamitocin yakin neman zaben.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 + 2 =