Hukumar NEMA ta raba kayan tallafin ambaliya a Jigawa

53

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta raba kayayyakin tallafi ga wasu al’ummomi 23 da suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwa a yankin karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

A jawabin da ya gabatar lokacin kaddamar da rabon kayayyakin, wakilin hukumar Malam Sa’idu Abdullahi ya ce hukumar ta basu tallafin ne domin rage musu radadi asarar da suka yi sakamakon ambaliyar.

Shima a jawabinsa mataimakin shugaban karamar hukumar, Alhaji Mustapha Yandutse wanda kuma shine ya kaddamar da rabon kayayyakin ya godewa hukumar da gwamnatin jihar Jigawa bisa kulawa da rayuwar wadanda suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwa a yankin.

Sauran wadanda suka yi jawabi sun hadar da sakataren mulki na karamar hukumar Alhaji Sabo Wada. Kayayyakin da aka raba sun hadar da bandiran kwanon rufi da katifu da man girki da gidan sauro da kuma kayayyakin abinci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + eight =