Gwamnonin G5 na PDP sun halarci gangamin yakin neman zabe

80

Jam’iyyar PDP jiya a jihar Abia ta kaddamar da gangamin yakin neman zabenta domin babban zaben 2023, inda ta tabbatar da alkawarinta na shugabanci bisa adalchi.

Gwamnonin G5 da Nyesom Wike na Rivers da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Seyi Makinde na Oyo da Samuel Ortom na Benue, na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.

Da yake jawabi a wajen taron a Umuahia, babban birnin jihar, Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia, ya bukaci mutanen jihar da su zabi jam’iyyar PDP domin tabbatar da dorewar ayyukan cigaba da shugabanci nagari.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa ‘yan takarar jam’iyyar za su samu nasara a zabukan saboda mutane ne masu nagarta kuma nasarorin da gwamnatin jihar ta samu karkashin mulkinsa.

A nasa jawabin, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, ya bukaci mutanen Abia da su jajircewa wajen goyawa jam’iyyar baya tare da tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ta yi nasara a babban zaben 2023.

A wani labarin kuma, wasu jiga-jigan ‘yan siyasar Arewa sun nisanta kansu daga wata kungiya karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, wacce ta amince da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023.

Wata kungiya da ke ikirarin ta kunshi wasu ‘yan siyasa Kiristocin Arewa, karkashin jagorancin Babachir Lawal, ta amince da Peter Obi a matsayin dan takararta a zaben 2023.

A wata sanarwa da ta fitar a Abuja, Babachir Lawal, ya ce kungiyar ta amince da Peter Obi ne, bayan nazari mai zurfi da bincike kan masu neman tikitin takarar shugaban kasa.

A cikin wata sanarwa da suka fitar jiya, wasu daga cikin ‘yan siyasar da suka hada da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, sun nisanta kansu daga kungiyar, inda suka ce Babachir Lawal ya yi magana da yawunsa ne kawai ba na kungiyar ba.

Wadanda suka sanya hannu kan sanarwar sun hada da Yakubu Dogara, da Simon Achuba, da Albert Atiwurcha, da Farfesa Doknan Sheni, da Mela A. Nunge, da Ishaya Bauka, da Farfesa Ibrahim Haruna da kuma Leah Olusiyi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 + 11 =