Gwamnatin tarayya ta mika aikin noman rani na Gari mai fadin hekta 228 ga manoma a jihohin Jigawa da Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Ban ruwa da magudanar ruwa na ma’aikatar albarkatun ruwa, Oyeronke Oluniyi, ya raba wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, yau a Abuja.
Ta ce aikin wani bangare ne na samar da abinci da ayyukan yi da gwamnati ke yi.
Oyeronke Oluniyi ya ce aikin noman ranin da aka mikawa manoma yana cikin kashi na shida, biyo bayan matakin da gwamnati ta dauka na kammala dukkan ayyukan.
Ta ce ma’aikatar, bisa manufarta ta noman rani, ta yi kafada da kafada da manufofin gwamnati mai ci na habaka tattalin arzikin kasa tare da fitar da mutane da dama daga kangin talauci kafin shekarar 2030.
Ta ce ma’aikatar ta dauki aikin masu ba da shawara domin gudanar da aiki mai inganci da kuma kula da tsarin noman rani.