Gwamnatin Kano za ta gyara makarantu 21

23

Gwamnatin jihar Kano ta fara shirin gyara makarantu 21 a fadin jihar.

Manajan Darakta na Hukumar Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano, KNUPDA, Suleiman Abdulwahab ne ya bayyana hakan a yau a lokacin da ya kai ziyarar duba wasu makarantun da ake gyarawa a babban birnin jihar.

Suleiman Abdulwahab ya ce an yi shirin ne domin ganin an gudanar da koyo da koyarwa cikin yanayi mai kyau

Ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne a matsayin martani ga jerin korafe-korafe da mahukuntan makarantar da mazauna gari suka yi na cewa a tsawon shekaru da suka wuce akwai kalubalen tsaro da batagari ke haifarwa a mafi yawan makarantun, da rashin ababen more rayuwa saboda karancin kudaden gyara makarantu da kuma karuwar yawan daliban.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa korafe-korafen sun kuma fito daga Kwamitin Gudanarwa na Makarantu da kuma na Iyayen Yara da Malamai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − nine =