Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Jigawa ta bude tayin bada ayyukan kwangila na gaggawa domin gina magudanan ruwa a unguwar Dan-masara da ke Dutse da kuma cikin garuruwan Babura da Kafin Hausa.
A jawabinsa wajen bude tayin bada ayyukan kwangilar, kwamishinan ma’aikatar, Alhaji Ibrahim Baba Chaichai ya ce gwamnatin jiha ta bada ayyukan kwangilar cikin gaggawa ne bisa la’akari da ambaliyar ruwan daminar bana wadda ta mamaye sassa daban daban na jihar nan.
Kwamishinan, wanda mukaddashin babban sakataren ma’aikatar, Lurwanu Abdulkadir Fanini, ya wakilta, ya ce an bada ayyukan kwangilar ne ta hanyar zabo kananan hukumomin Dutse da Babura da Kafin Hausa daga shiyoyi uku na jihar nan.
Ya bada tabbacin biyan kudaden ayyukan kwangilar a kan lokaci.
A nasa bangaren, wakilin hukumar kula da bada ayyukan kwangila na jihar Jigawa Injiniya Aminu Lawal ya bukaci kamfanonin da suka samu nasara su tabbatar sun yi aiki mai inganci.