Buhari zai kaddamar da sabbin takardun kudi a gobe

79

Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a gobe zai kaddamar da sabbin takardun kudi na naira dubu daya da 500 da kuma naira 200 da aka sakewa fasali.

Godwin Emefiele ya bayyana hakan ne a yau yayin taron kwamitin kula da harkokin kudi na bankin karo na 288 a Abuja.

Ya kuma kafe kan cewa bankin ba zai canza wa’adinsa na dawo da duk tsofaffin takardun kudi zuwa bankuna ba domin musanyawa da sabbi.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 26 ga watan Oktoba, babban bankin kasar CBN ya bayyana shirin fitar da takardar kudi na naira dubu daya da 500 da kuma naira 200 da aka sakewa fasali a ranar 15 ga watan Disamban 2022.

A cewar CBN, sabbin kudaden da ake da su za su ci gaba da kasancewa a kan doka kuma za a rika amfani da su tare da sabbin har zuwa ranar 31 ga Janairun 2023.

Sai dai Godwin Emeifele ya yi watsi da wa’adin, inda ya ce CBN din ba zai jira ba har zuwa ranar 15 ga watan Disamba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + eight =