An kulle dalibin da ya soki Aisha Buhari a gidan yari

24

Aminu Mohammed dalibin jami’ar tarayya dake Dutse, wanda aka kama bayan ya soki uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari a shafin Twitter, an tsare shi a gidan yarin Suleja dake jihar Neja.

A cikin watan Yuni, dalibin ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa Mama ta ci kudin talakawa ta yi bul-bul.

Bayan watanni da wallafawa, jami’an tsaro suka kama shi tare da garzayawa da shi zuwa fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda aka yi masa dukan tsiya da azabtar masa.

An tsare dalibin ne bayan an gurfanar da shi a gaban wata kotu da ke Abuja.

Da yake magana da BBC Hausa, lauyansa, CK Agu, ya ce kotu ta ki bayar da belin Aminu.

Aminu Mohammed wanda dan asalin garin Azare ne a jihar Bauchi, dalibi ne a ajin karshe a sashin kula da muhalli a Jami’ar Tarayya dake Dutse.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 + 14 =