Za a samar da mitar lantarki ga karin gidaje miliyan 6 – Osinbajo

23

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce ana kokarin samar da mitocin wutar lantarki ga karin gidaje miliyan shida a Najeriya.

Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron bibiyar ayyukan ministoci karo na 3 da aka shirya wa ministoci da manyan sakatarori da manyan ma’aikatan gwamnati, jiya a dakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja.

Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, shirin samar da mitocin zai yi matukar tasiri wajen samar da wutar lantarki a fadin kasar nan.

Mataimakin shugaban kasar ya ce daya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin ta samu shi ne a bangaren tattalin arzikin zamani.

Ya ce bangaren ya ba da gudummawar kashi 18.4 bisa 100 ga ma’aunin tattalin arziki na GDP a tsakiyar shekarar 2020, wanda ya kasance mafi girma da aka taba samu a tarihin kasar, kuma kusan ninki uku na abinda aka samu a bangaren mai da iskar gas.

Mataimakin shugaban kasar ya ce fara amfani da fasahar 5G zai bayar da babbar gudunmawa ga tattalin arzikin zamani a Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 2 =